Hanyoyin kyautata damar samun aiki a Jamus
Masu neman hazikai a Jamus na yawaita yin korafi a kan abu guda kusan kullum. Ga kadan daga cikin dabarun samun nasara ga mai neman aiki da ka iya taimaka wa mai bukata. Ba dai sabon abu ne ba, amma kuma kada a raina.
Abin yi: A nemi ayyuka na kwarai
Karanta bayanai kan nau'in aiki da kake muradi don tabbatar da sun dace da abin da kake nema. Idan ba ka jima da kammala karatu ba, kada ka nemi matsayin shugaban kamfani ko ma'aikata. Sai dai kuma kada ka kaskantar da kanka. Kamfanonin na samun masu neman aiki da yawa, shi ya ba sa wuce minti biyar wajen ganawa da mai bukata. Idan ka gaza gamsar da su, bukatarka na iya shiga kwandon shara.
Abin kiyayewa: Aikawa da takardun neman aiki da ba su kammala ba
A tabbatar da samar da dukkanin abubuwan da aka bukata cikin sanarwar neman aiki. A kullum a kintsa takardu ta yadda ba za a tashi nema a kasa samunsu ba. Za ka bukaci kwafin takardun bayanan da suka shafi asalinka da karatunka daga matakin farko har zuwa jami'a ko makamancin haka, da wasu muhimman mutanen da za a tuntuba don karin haske a kanka, wadanda duk su ne za su tabbatar da cancantarka.
Abin yi: A yi kokarin tabbatar da bin tsari
Koda yake hikimar kirkira na da kyau, akwai wasu tsare-tsaren Jamus da suka kamata a lura da su wajen tsara takardun neman aiki. Misali sai an sanya lokacin da aka haifi mutum da kuma hoton fasfo. Hotuna na da tasiri sosai a tsarin neman aiki a Jamus. Ba bu dai tsanantawa a yanzu, amma akasarin kwararru masu daukar aiki na son ganin ko da guda don ba su damar tsara takardu dalla-dalla.
Abin kiyayewa: A fayyace karara wanda za a aika wa takardun neman aiki
Ba daidai ba ne aika takardun neman aiki zuwa ga misali, ''Yallabai ko Hajiya ko Malama' ko kuma "To whom it may concern". A gudanar da bincike ta yanar Intanet don sanin shugaban sashin da ke daukar aikin. Yin hakan na tabbatar da sha'awarka ga aiki. Ana iya amfani da kafofin zamani irinsu LinkedIn ko XING don samun wanda ake nema. Haka ma a sanya adireshin ma'aikatar a kan takardar neman aikin.
Yi amfani da hanyoyin gyaran tsari na rubutu mai kyau
Masu daukar aiki ba su bata lokacin kan rubutu mai kura-kurai. Ana iya kauce wa hakan wajen bincika harafi ko kalma da kyau kafin a rubuta. Abu ne mai sauki. Wasu sassan kula da harkokin ma'aikata kan soke sunan duk wani mai neman aiki da ya yi kuskure a rubutu. koda yake akwai wadanda ke iya barin kananan kura-kurai, amma hakan na iya rage kimar mai bukatar aikin.
A nemi shawarwari masu kyau
Zai yi kyau a nemi taimako ko kuma shawara, musamman idan mai neman aiki ba mazaunin Jamus ko Bajamushe ba ne. A bai wa wani ya karanta, sannan a nemi shawararsa ko da kuwa ka rubuta takardun bayananka cikin Ingilishi, takardar shaida da wani zai yi kanka na iya kasancewa cikin Jamusanci. Ana iya gane cewar an taimake ka, sai dai hakan ya isa ya nuna irin kokari da ka yi wajen tsara takardunka.
A tabbatar da bayanai na hakika
Shirga karya a takardun neman aiki ba dabara ba ce. Babu karya, kawai a kware. Yanzu a Jamus masu daukar aiki ba sa damuwa da siffa ko launin jikinka. A shekarun baya dai ba a daukar masu zane ko huda jikinsu, balle su fito a ma'aikatu. Amma a yanzu hatta 'yan sanda kan nuna zanen jiki da suke yi yayin da suke bakin aiki. Hakan na tabbatar da sauyi ne da karancin kwararrun ma'aikata da ke a Jamus.
A tsaya kaifi daya
Tabbata ka tsara jadawalin bayananka da kyau. Haka ma yake ga takardarka ta gabatar da mai nema. Muhimmin abu ne a bi tsarin rubutu irin su kwanan wata da inda aka haifi mutum da dai muhimman bayanai yanda ya kamata, don dukkaninsu ne mai daukar aiki ke fara gamuwa da su, hakan kuwa zai dauke ka. Ka sani ba a bukatar shafukan bayananka masu yawa muddin kana iya gamsar da mai daukar aiki a takaice.
A kula da abubuwan da ake yadawa ko aikatawa a shafukan Intanet
Wannan wani darasi ne mai kyau a rayuwarka, sai dai galibi ana watsi da shi, musamman ga masu wallafa hotunansu na maye ko masu harzuka jama' ko na badala. Kaddara, shugabanka na bibiyar abubuwan da kake wallafawa a shafukanka. Muhimmin abu ne ka samar da bayanai a shafukanka, wadanda za su bayyana ka a matsayin mutumin da ya dace da ma'aikaci da za a yarda da shi don yin aiki da shi.