1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Hanyoyin inganta lafiya a Afirka

November 9, 2023

Nazarin 'yan majalisun dokokin kasashen Afirka daga darusa na abin da aka gani a lokacin annobar Corona da kuma cutar Ebola

https://p.dw.com/p/4YbjP
Kanana, Hammanskraal, Südafrika | Cholera-Ausbruch
Hoto: Shiraaz Mohamed/AFP

Wannan shi ne karon farko da hukumar lafiya ta duniya WHO ke shirya taro mai muhimmanci da ‘yan majalisu na kasashen Afirka musamman don tsara dabarun shawo kan annoba idan ta auku musamman matakan da gwamnatocin nahiyar za su dauka domin dakile ta cikin gaggawa.

Watanni biyu da suka gabata shugabannin kasashen duniya sun amince da shawarwari kan hanyoyin tunkarar annoba a taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a birnin New York na kasar Amurka.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dr. Tedros Ghebreyesus ya ce  wajibi ne ‘yan majalisun kasashen Afirka su tabbatar gwamnatocinsu sun cika wannan alkawari.

Tedros Adhanom Ghebreyesus shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO
Tedros Adhanom Ghebreyesus shugaban hukumar lafiya ta duniya WHOHoto: Esa Alexander/REUTERS

"A matsayinku na ‘yan majalisu, kuna da matsayi na musamman da za ku tabbatar da alkawuran da gwamnatoci suka dauka kan wannan batu sun tabbata gaskiya. Hukumar lafiya duniya na tabbatar muku cewa za ta goyi bayanku domin ganin kun cimma haka. Lamarin na da muhimmanci musamman ga nahiyar Afirka, inda ake da matsalolin da ke hana cimma wadannan muradu da ke da alaka da rashin hada hancin bukatu daga bangarori da dama.”

Karin Bayani: WHO ta bukaci hadin kai don yaki da annoba

Annoba kamar Ebola da Corona da aka gani a baya, sun yi ta'adi kwarai da gaske a nahiyar Afirka da sauran sassan duniya, matsalolin da suka durkusar da fannonin lafiya masu yawan gaske.

Wannan taro da daruruwan ‘yan majalisun na Afirka ke yi a Accra babban birnin kasar Ghana, na fatan maganin duk wata tawaya a asibitoci musamman a lokacin da aka fi bukatar su.

Jagorar WHO ta shiyyar Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta ce akwai kwarin gwiwa gami da fata daga yadda aka shawo kan annobar Corona a nahiyar.

Yaki da annobar Ebola a Uganda a shekara ta 2000
Yaki da annobar Ebola a Uganda a shekara ta 2000Hoto: Luke Dray/Getty Images

"A farko-farkon lokacin annobar Corona, gwamnatocin kasashen Afirka tare da taimakon majalisun dokokinsu sun tashi tsaye domin ganin sun kare al'umomi da tattalin arzikinsu. Kuma daukar shawarwari cikin lokaci, ya taka rawa kwarai wajen kauce wa mace-macen da aka yi hasashen za a gani a nahiyar.”

Karinn Bayani: Hukumar Lafiya ta Duniya: Taro kan Ebola

Ministan lafiya a Ghana, Agyemang Manu ya yarda cewa cimma manufar tsarin kula da lafiya mai nagarta a nahiyar Afirka, abu ne da ke bukatar ‘yan majalisu su samar da dokoki da kudade na daukar nauyinsu.

"Dole mu dage domin maganta rashin daidaiton da ake da shi a bangaren samun kulawa ta lafiya a tsaknin mutanen da muke wakilta. Matsayinmu a bangaren samar da dokoki, da amince wa da kasafin kudi da sa ido kan yarjejeniyoyin cikin gida da waje suna da muhimmanci ga cimma wannan manufa ta ingantacciyar lafiya .”

‘Yan majalisun Afirka a taron na Ghana, sun nuna alamu tare da tabbatar da cewa da gaske suke yi na ganin an inganta fannonin lafiya a kasashensu, duk da cewa akwai miliyoyin ‘yan Afirka da ke ganin an jima ana ruwa kasa tana shanyewa.