WHO ta bukaci hadin kai don yaki da annoba | Labarai | DW | 19.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta bukaci hadin kai don yaki da annoba

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta bukaci kasashe su kara himma wajen kare lafiyar jama'arsu daga barazanar annobar cutattuka.

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ta bukaci kasashe su kara azama wajen kare lafiyar jama'arsu daga barazanar annobar cutattuka da kuma ka iya kaiwa ga haifar da koma bayan tattalin arziki.

Babbar daraktar kungiyar lafiyar ta duniya Margaret Chan ta baiyana haka a taron ministocin lafiya na kungiyar kasashe ashirin masu cigaban masana'antu na duniya G20 da ya gudana a birnin Berlin.

Ita ma da take tsokaci shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kira ta yi ga kasashen masu ci gaban masana'antu su taimaka da kudade wajen samo sabbin hanyoyin yaki da annobar cutattuka.

Ta ce akwai bukatar mu kara kaimi yadda matakan da muke da su za su yi tasiri a nan gaba. Domin cimma wannan muna bukatar yin taka tsantsan wajen amfani da magungunan Antibiotics yadda kwayoyin cuttukan ba za su bijirewa maganin su cigaba da yaduwa cikin hanzari ba,