Hama ya amince da matakin kotu na watsi da takararsa | BATUTUWA | DW | 11.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Hama ya amince da matakin kotu na watsi da takararsa

Madugun 'yan adawar Nijar ya sanar da shigar jam'iyyarsa a sauran zabukan da ke tafe, tare da kulla kawance da wani dan takarar shugaban kasa don kwace mulki a hannun PNDSA Tarayya.

Hama Amadou

Hama Amadou madugun 'yan adawar Jamhuriyar Nijar

Da farko dai madugun ‘yan adawar na NijarHama Amadou ya amsa a fakaice da karbar matakin kotun tsarin mulki na yin watsi da takararsa a zaben shugaban kasa, amma kuma  ya ce ko ta wani yanayi mahukunta suka shirya sauran zabukan ba makawa jam’iyyarsa za ta shiga a fafata da ita inda ya ce "Ana tsammanin dakatar da takara ta a zabe zai sa jam'iyyar Lumana Afirka ta mutu, saboda haka ina son jama'a su gane ko da ba zan shiga zaben shugaban kasa ba amma muna da 'yan takara a zaben majalisar dokoki da kananan hukumomi, saboda haka a kada masu kuri'a."

Karin Bayani:Kotu a Nijar ta hana madugun adawa takara

Yiwuwar goyon bayan wani dan takara

Wahlplakat für Hama Amadou Niger

Hoton dan takarar jam'iyyar adawa

Duk da yake cewa Jam'iyyar Lumana Afrika ba ta da dan takara a zabebn shugaban kasa tun bayan da kotun tsarin mulki ta yi watsi da takarar Hama Amadou, Madugun ‘yan adawar ya ce jam’iyyarsa za ta kama wa wani daga cikin ‘yan takarar daga kawancen jam’iyyun adawa wanda jam’iyyar za ta bayyana a nan gaba idan lokacin bayyana hakan ya yi, yana mai cewa "Sai sun yi shawara tare da tuntubar juna a cikin jam'iyyar takwana kafin daukar wannan mataki."

Karin Bayani: Ana shirin zabe cikin rudanin siyasa a Nijar

Innenminister von Niger

Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya

Da yake tsokaci kan babban abokin hamayyarsa dan takarar jam’iyya mai mulki Bazoum Mohamed, Malam Hama Amadou ya jaddada shakkunsa a kan ingancin takardun dan kasa na dan takarar na jam’iyyar PNDS Tarayya tare kuma da mayar da martini a kan wani zargi da ya ce ya yi masa kan batun abin da ya kira takardun boge da y ace  kotun tsarin mulki ta gano a cikin takardun takarar Malam Bazoum Mohamed.

Karin Bayani: Bazoum ya kayar da 'yan adawa a kotun Diffa

Sai dai Hama Amadou ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da kalubalantar takardun takarar Malam Bazoum Mohamed a gaban kotun tsarin mulki har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.