Nijar: ′Yan adawa za su yi karar Bazoum | Labarai | DW | 29.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijar: 'Yan adawa za su yi karar Bazoum

Gamayyar jam’iyyun adawar Nijar na FRDDR sun sanar da aniyarsu ta shigar da kara kotu sakamakon samun wasu 'yan siyasa da amfani da kayan gwamnati wajen yakin neman zabe ciki kuwa har da ministan cikin gida.

Gamayyar jam'iyyun adawar sun shirya don karar Bazoum Mohamed ministan cikin gidan kuma mai takarar shugabancin kasar a jam’iyya mai mulki sakamakon fita rangadin siyasa da kayan gwamnati kafin zabe.

Malam Rabi'u Gwanda guda daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyun adawar kasar ta Nijar ya bayyana saba ka'idar da dan takarar shugabancin kasar ya yi a matsayin dalilinsu na daukar matakin shari'a.