Hama Amadou: Murna ta koma ciki | Siyasa | DW | 18.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hama Amadou: Murna ta koma ciki

Madugun 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya sake gabatar da kansa a gaban kotu inda kotu ta sake mayar da shi a gidan yari domin cika ragowar wa'adin watanni takwas da suka rage masa.

Kamar yadda dawowar madugun 'yan adawa Hama Amadou ta zo wa jama'a ba zata, haka kuma komawar madugun 'yan adawa Hama Amadou a gidan yarin Filingue mai tazarar kilomita akalla 200 daga babban birnin Yamai ya zo da ba zata ga jama'a.

Da sanyin safiyar ranar Litinin ne madugun adawar ya kai kansa a gaban shari'a, kwanaki bayan ya soma zaman makokin da ya dawo da shi a gida inda bangarorin siyasa dabam-daban suka tattauna da shi a gidansa don yi masa ta'aziya sakamakon rasuwar mahaifiyarsa a farkon watan Nuwamba na 2019.

Komawar madugun na 'yan adawa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin siyasar kasar Nijar na adawa da na bangaren masu mulki a yayin da ake gabanin manyan zabukan kasar, wanda masu sharhi ke ganin yiwar yiwa madugun na 'yan adawa ahuwa ko da kuwa yana da sauran wa'adin da bai kara kammalawa ba a gidan yari na tsawon watanni takwas.

Sai dai masu nazarin al'amuran siyasa na ganin matakin yin ahuwar bai kamata ya shafi Hama Amadou kadai ba da kotu ta zarga da aikata laifin safarar jarirai daga Najeriya, har ma da wasu wadanda tuni suka yi zaman gidan yari da sauran jama'ar da laifukansu kan batun bai yi wani muni fiye da kima ba.

Mai shekaru 69 a duniya madugun 'yan adawar Nijar Hama Amadou ya koma gida ne a ranar 14 ga watan Nowamba, bayan ya shafe tsawon shekaru yana gudun hijira a kasashen waje wanda ya soma tun a cikin watan Maris na shekarar 2016.