Halin rashin sanin tabbas a Ukraine | Labarai | DW | 27.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Halin rashin sanin tabbas a Ukraine

Har yanzu ana cikin yanayi mai rudani a gabashin Ukraine dangane da kutsen da ake zargi sojojin Rasha sun yi a cikin motocin yaki.

Gwamnatin Rasha ta yi alkawarin ba da cikakken hadin kai da kungiyar agaji ta Red Cross da kuma hukumomin birnin Kiev game da kayan agajin da Rashar ke son tura wa gabashin Ukraine. Rahotanni daga fadar Kremlin a birnin Mosko sun ce shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Petro Poroshneko sun amince da wasu jerin matakai a taron da suka gudanar ranar Talata a birnin Minsk na kasar Belarusia. Sai dai kawo yanzu bangaren Ukraine bai tabbatar da wannan labari ba. Yanzu haka dai ana cikin halin rashin tabbas a gabashin Ukraine. Wani kakakin sojin kasar ya ce wani gungun sojojin Rasha sun kutsa yankin kudu maso gabashin kasar cikin motocin yaki da na daukar kaya. A fadan da aka yi a arewacin yankin sojoji sun kashe 'yan aware kimanin 200 sannan sun lalata motoci masu sulke da kuma rokoki da yawa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu