1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwace iko daga hannun 'yan tawayen Tigray

Suleiman Babayo AMA
November 30, 2020

Gwamnatin Habasha ta bayyana kwace iko da yankin Tigray yayin da ake ci gaba zaman zullumin rashin sanin hakikanin abin da ke faruwa bayan katse layukan sadarwa da hanyoyin shiga yankin.

https://p.dw.com/p/3m1l5
Tigray-Konflikt | Militär Äthiopien
Sojojin gwamnatin Habasha na murnar karbe iko a TigrayHoto: Ethiopian News Agency/AP/picture alliance

Firamnista Abiy Ahmed na Habasha ya jinjina wa dakarun kasar cikin fafatawa da 'yan tawayen Tigray inda ya ce duk matakan kare fararen hula dakarun sun dauka kuma tuni sun samu galaba kan mayakan 'yan awaren na kungiyar TPLF. A karshen mako gwamnatin Habasha ta aiyana kwace iko da babban birnin yankin Mekelle bayan da sojojin gwamnatin suka kaddamar da farkoki. Firaminista Abiy ya tabbatar wa 'yan kasarsa cewa sojoji ba za su lalata birnin ba.

Äthiopien | Videostill Ethiopian News Agency | Militär
Sojojin kasar Habasha a shirin ko takwanaHoto: Ethiopian News Agency/AP Photo/picture alliance

Zadig Abraha minista mai kula da harkokin dimukaradiyya ya ce dole ne gwamnati ta hana 'yan jarida da sauran jami'ai shiga yankin sakamakon yanayin da ake ciki. "Ba mu ne ke toshe komai ba yanayin da ake ciki ne, akwai aiyuka na soja wannan ka iya zama hadari ga rayuwa, a lokaci guda 'yan ware sun kaste layukan waya, sun lalata hanyoyin da filayen jiragen sama. Muna aiki sake ginawa. Idan babu wadanann abubuwa ba wanda zai iya shiga samun wani bayani, ba abin da muke boyewa."  Daruruwan mutane sun halaka yayin da dubban suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin na kusan wata guda.

Karin Bayani: Murkushe 'yan aware da karfin tuwo a Habasha

Jagoran 'yan waren Debretsion Gebremichael na yankin na Tigray ya nemi gwamnatin Habasha ta dakatar da abin da take yi na rashin tunani kuma suna nan kusa da babban birnin yankin Mekelle inda suke ci gaba da fada. Ya fadi haka yayin hira da kamfanin dillancin labaran AP sannan Gebremichael mai shekaru 57 da haihuwa ya musanta rahoton ya tsere gudun hijira zuwa Sudan ta Kudu.

Karin Bayani: Kyautar Nobel ga Abiy Ahmed

Äthiopien Ministerpräsident Abiy Ahmed Ali
Firaministan Habasha Abiy Ahmed Hoto: Office of the Prime Minister/Reuters

'Yan waren sun fusata da matakin Firaminista Abiy Ahmed na rage tasirin yankin ta mayar da yawan dakaru zuwa kashi daya cikin hudu, maimakon kashi 60 cikin 100 da suke da shi gabanin ya dauki madafun iko, kana suna ganin gwamnatin kasar duk matakan da take dauka na tsangwama musu ne. Ita dai Tigray People's Liberation Front (TPLF) a baya ke rike da madafun ikon Habasha kimanin shekaru 30 har zuwa shekara ta 2018.