1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Habasha za su murkushe 'yan aware

Usman Shehu Usman LMJ
November 26, 2020

Firaminista Abiy Ahmed ya bai wa sojojin kasar Habasha damar kaddamar da hare-hare na karshe, domin murkushe 'yan waren Tigray da ke yankin arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3lsaQ
Äthiopien | Premierminister | Abiy Ahmed Ali
Hoto: Michel Euler/REUTERS

Firaminista Abiy Ahmed ne ya sanar da hakan, jim kadan bayan cikar wa'adin sa'o'i 72 da ya dibar wa 'yan awaren na Tigray People's Liberation Front (TPLF), na su mika wuya su kuma kawo karshen tawayen da suke yi. Abiy dai ya bayyana a shafinsa na sada zumunta na Facebook cewa, dubban 'yan aware na Tigray sun mika wuya cikin wa'adin na sa'o'i 72 da ya dibar musu, wwanda hakan ke nuni da cewa hare-haren da ya bai wa sojoji umarnin kai wa, za a kai su ne kawai a kan wadanda suka bijirewa umurnin gwamnati. 

Karin Bayani: Firaminista Abiy ne ya janyo rikici?

Firaministan ya tabbatarwa da mazauna yankin cewa, za a dauki kwararan matakai domin tabbatr da hare-haren ba su shafi fararen hula da wuraren gudanar ibadu da gidajen tarihi da kuma ababen da suka shafi rayuwar al'umma ba. Haka kuma ya bayyana cewa gwamnati za ta dauki matakin bayar da agaji domin tabbatar da ganin ta tallafawa dukkan wadanda ke bukatar taimako, kana a shirye take ta taimaki dukkanin al'ummar kasar ta Habasha da suka yi gudun hijira, domin su koma yankunansu na asali.
Sai dai kungiyar Amnesty International ta nunar da cewa zai wahala hare-haren su gaza rutsa wa da fararen hula da sauran wuraren da ya ambata, domin za ayi amfani da jirage da tankokin yaki wadanda ke harba rokoki a birnin da ke da mazauna sama da rabin miliyan. Su ma dai mayakan na Tigray an zargesu da kisan kiyashi, bayan da aka samu kaburburan da aka binne mutane. Ganau sun ce a kalla mutane 600 aka halaka, wadanda ba 'yan kabilar Tigray ba ne. Daniel Bekele shi ne shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Habasha, ya kuma ce: "Su da kansu sun  fara aikita laifi a yankin nasu. An tarar da tarin kaburbura a yankin da kuma gawarwaki a wurare masu yawa. Abin da aka gani an samu shaidarsa ne daga iyalai da 'yan uwan wadanda aka halaka"

Äthiopien | Menschen fliehen aus der Tigray Region
'Yan gudun hijirar Habasha na tagayyaraHoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Karin Bayani: 'Yan Habasha na tserewa zuwa Sudan.

Ita ma kungiyar Amnesty International ta tabbatar da labarin kisan gillar, sai dai babu tabbas wane bangare ne ya aikata. A yanzu dai akwai dubban 'yan gudun hijira, inda tun gabanin isar dakarun gwamnati daruruwan al'ummar ta Habasha suka tsallaka zuwa kasar Sudan da ke makwabtaka da ita. A sansanin 'yan gudun hijira na Um Rakouba da ke kasar ta Sudan, wanda a shekarun 1980 ya tsugunar da 'yan Habsha da annobar tamowa ta koro, akwai dubban 'yan gudun hijirar ta Habasha. Kungiyar Tarayyar Afirka dai ta tura tauwagar shiga tsakani, domin yayyafa ruwa kan rikicin, to amma Firaminista Abiy wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel a shekarar da ta gabata, sakamkon wanzar da zaman lafiya tsakanin kasarsa da makwabciya Iritiriya, ya yi fatali da wannan tayi. Tun dai a farkon wannan wata Abiy ke fukantar gagarumin kalubale, bayan da ya bai wa sojoji umurnin kawo karshen ayyukan 'yan awaren na TPLF.