1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Dubban mutane na hijira zuwa Sudan

Abdoulaye Mamane Amadou
November 11, 2020

A daidai lokacin da dakarun gwamnatin Habasha ke ci gaba da yin artabu da na 'yan tawayen yankin Tigray, dubban mutane daga yankin Tigray na tserewa zuwa kasar Sudan don neman mafaka.

https://p.dw.com/p/3l9RM
Äthiopische Tigray-Migranten
Hoto: picture-alliance/AP Images/N. El-Mofty

Gidan talabijin din Habasha na nuna hotunan hare-haren jiragen yakin kasar a kan yankin Tegray, kafin tura samamen sojan kasa da suka yi artabu da mayakan 'yan tawayen yankin, lamarin da ya jawo salwantar rayukan gwamman mutane daga bangarorin biyu.

Janar Ridhwan Husain jagoran kai hare-haren jiragen yakin ya bayyana hare-haren a matsayin na rigakafi yana mai cewa 'yan tawayen yankin na Habasha da ke Tigray sun mallaki muggan makamai."Suna da rokoki masu cin dogon zargo wadanda za su iya isa ko ina a kasar nan har da makwabta dalilan da suka sa muke kaddamar da harin da nufin wargaza makaman."

Bildergalerie Flüchtlingscamp Tigray in Äthiopien
Sansanin 'yan gudun hijira a Tigray a HabashaHoto: Milena Belloni

Tuni dubban mutane suka tsere daga gidajensu suna tsallakawa zuwa kasar Sudan don samun mafaka, Ahmad Abdulgany jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijira a Sudan ya ce 'yan Habasa 200.000 ne suka samu mafaka a kasar yana mai cewa yanzu hakan kasar na cikin yanayin tsugunar da jama'ar yana mai bayyana cewa za su fusknaci matsloli muddin ba su samu dauki daga Majalisar Dinkin Duniya ba.

Karin Bayani: Fargabar barkewar yaki da Tigray

Äthiopien Premierminister Abiy Ahmed
Hoto: Minasse Wondimu Hailu/picture alliance/AA

Firaiministan Habasha da ya samu lambar yabo ta Nobel, ya bayyana hare-haren a matsayin na samar da zaman lafiya maimakon na murkushe yan adawa ko tawaye ba. "Tun shekaru biyun da suka gabata, burin wadannan masu ta da kayar bayan shi ne jefa kasarmu cikin yamutsi da zaman kara zube. Sun ki aminta da matakan duk wata tattaunawa, saboda burin su ba cimma zaman lafiya ba ne, so suke su kare mahandama da maciya amanar kasa, da kuma dawo da tsarin mulkin bangaranci da na kabila dana addini." 

To sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'Adama na zargin samamen dakarun gwamnatin ke kai na ritsawa da talakawan yankin da ba su san hawa ko sauka ba, a yayin da manyan masu fada aji tun bayan zaben yanki Tigray ke tsallakewa zuwa ketare suna zuga matasa da suci gaba da tayar da kayar baya, lamarin dake barazanar jefa kasar cikin yakin basasar da ba a san karshensa ba.