Abiy ya ki tattaunawa da ′yan Tigray | Labarai | DW | 27.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Abiy ya ki tattaunawa da 'yan Tigray

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya sake tuburewa a kan batun tattaunawa da shugabannin 'yan tawayen yankin Tigray. Sai dai ya ce a shirye yake ya yi magana da wakilan kungiyar da ke aiki bisa doka da oda.

Abiy ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya ke ganawa da wasu wakilai uku daga Kungiyar Tarayyar Afirka, a kokarinsu na kawo karshen  rikicin da ake tsoron zai iya mamaye yankin gaba daya.

Dubban mazauna Tigray ne ke ci gaba da tserewa daga yankin, bayan cikar wa'adin da Abiy Ahmed ya bai wa mayakan fafutukar da su mika wuya ko sojojin gwamnati su kai sumamen karshe na murkushe su.

Da alama dai wannan matakin bai yi wa wakilai na musamman na AU da suka hada da tsoffin shugabannin kasasahen Laberiya Ellen Johnson Sirleaf da na Mozambik da kuma na Afirka ta Kudu dadi ba.