1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rikici na kamari tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Tigray

Ramatu Garba Baba AMA
November 5, 2020

Bayan umarnin firaministan Habasha Abiy Ahmed na kaddamar da hari kan bangaren adawa na Tigray, rikici ya rincabe tare da ci gaba da tafka asarar rayukan jama'a.

https://p.dw.com/p/3kvI6
Äthiopien Militärparade in Tigray
Hoto: DW/M. Hailesilassie

Fada ya barke a tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawaye a yankin arewacin kasar Habasha, bayan umarnin Firaiminista Abiy Ahmed na tura rundunar sojin gwamnati  a matsayin martini kan harin da bangaren adawa na Tigray People’s Liberation Front TPFL ta kai wa sansanin sojin kasar inda aka tafka barnar rayuka da dukiya, gwamnatin Habashan ta ce laifi ne babba na cin amanar kasar, a jawabin mataimakin firaminista Demeke Huseein ya nemi hadin kan yan kasa a daidai wannan lokacin. 

Tun bayan yin gaban kansa na gudanar da zabe a watan Satumba da yankin Tigray na arewacin kasar ya yi mahukuntan Habashan sun danganta hakan a matsayin nuna tirjiya ga umurnin framinista Abiy Ahmed tare da haifar da zaman doya da manja, kuma a cewar masanin siyasar kasa da kasa irin su William Davison ya ce ana bukatar matakin gaggawa don shawo kan rikicin, inda yace "A wannan gabar babu bukatar a sa ido a fadan har ya ci gaba da rincabewa, a dauki matakin ganin an tsagaita bude wuta daga bangaren gwamnati da na Tigray, sannan a gaggauta hawa teburin sulhu don tattauna mafita daga rikicin." 

Karin Bayani: Ra'ayin 'yan Habasha kan salon mulkin Abiy

Majalisar Dinkin Duniya ta baiyana damuwarta tare da yin kira na a dakatar da fadan Stephane Dujarric mai Magana da yawun Sakataren Majalisar yace sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a kawo karshen rikicin ya kuma kara jadadda goyon bayan majalisar ga gwamnatin kasar Habasha a kokarin ganin a gina kasa an samar da abubuwan ci gaba tare da mayar da ita kan turbar zaman lafiya da walwala ga dukkan al’umma baki daya.

Kasashen Somaliya da Sudan da ke makwabtaka da Habasha sun fada cikin rudani da yanayi na rashin tabbas a yayin da bangaren adawa na Tigray People’s Liberation Front TPFL, ke cewa sun kashe sojojin gwamnatin Habasha da dama.