1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dinke baraka a tsakanin Habasha da Iritiriya

Ramatu Garba Baba ZU/MNA
July 9, 2018

Ana fata wannan mataki zai kawo karshen jayayya na fiye da shekaru 20 da kasashen Iritiriya da Habasha suka kwashen suna yi.

https://p.dw.com/p/315Tr
Eritrea Treffen Abiy Ahmed und Isaias Afwerk  in Asmara
Hoto: picture-alliance/dpa/ERITV

Shugabannin kasashen Habasha da Iritiriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Asmara, babban birnin kasar Iritiriya. Matakin da ake ganin zai kawo karshen jayayya na fiye da shekaru 20 a rikicin mallakar ikon filaye da ya lakume rayukan dubban al'ummar kasashen biyu. A ganawar shugabanin biyu, sun dauki alkawarin juyawa sabanin baya don samar da ci gaban da 'yan kasa za su ci gajiyarsa.

Shugabannin biyu sun soma da daukar matakin bude hanyar sadarwa da aka yanke na tsawon lokaci a tsakaninsu tare da daukar alkawarin bude ofishin jakadancinsu a kasashen juna. Daga nan sun gana bayan sun sha hannu cike da murmushi inda aka taresu da raye-raye irin na al'adun gargajiya. Shugaba Isaias Afwerki na kasar Iritiriya shi ya soma jawabi bayan da ya jinjina wa takwaransa. Ya ce tabbas an tafka asara na rai da dukiya wanda ba za a iya maido su ba amman kuma yanzu lokaci ya yi da za su juyawa wadannan munanan batutuwan baya.

Jinjina ga namijin kokari

"Yanayin da dakta Abiy ya samar, yanayi ne mai darajar gaske, shakka babu, farin cikin al'umma bai kwatantuwa. Asarar da muka yi a shekaru 25 da suka gabata ba sa misultuwa, amman yau, sai muka gani kamar babu abin da muka rasa, mun ji tamkar mun yi nasarar gano wani abu mai mahimmanci da ya sullube mana ne."

Äthiopischer Ministerpräsident Abiy Ahmed beim Staatsbesuch in Eritrea
Hoto: Twitter/@fitsumaregaa

Jama'ar da ke zauren sun ci gaba da yin tafi wasu na guda suna jinjinawa shugabannin biyu. Ko da lokacin na shi jawabin ya zo, Firaiministan Habasha Abiy Ahmed, bayan bayyana farin cikinsa ya yi waiwaye kan illolin da rikicin na tsawon lokaci ya haifar. Daya daga ciki shi ne yadda yakin ya tilastawa dubban jama'a tserewa daga kasashensu na asali, abin da ya sa ya kuma jaddada zaman lafiya kadai a matsayin mafita.

"Idan da zaman lafiya a tsakanin Habasha da Iritiriya, yankin kahon Afirka ma zai zauna lafiya, zai kuma samu bunkasa. Yanzu al'ummarmu na nan a warwatse a sassan duniya a matsayin 'yan gudun hijira. Muna fatan yanzu za su dawo gida, ba za a sake ci gaba da safarar al'ummarmu kamar kayayyakin masarufi ba.''

Fatan kawo karshen rikici

Zaman sulhun a sanadiyyar yunkurin da shugaban na Habasha mai cike da fatan samar da sauyi ya soma yi ne, wanda kuma ake ganin ba wai zai tsaya ba ne ga kawo karshen rikicin mallakar kan iyaka kadai, amma mataki ne da zai kawo karshen yadda aka mayar da kasashen biyu saniyar ware a yankin. Za a iya fahimtar hakan idan aka yi la'akari da kalaman karshe a ganawar da shugaban Iritiriya Afwerki ya yi da cewa:

"Na jinjina maka dakta Abiy. Muna tare a wannan tafiya, za mu fuskanci duk wata barazana tare, muna tare a wajen nema, za mu kuma yi nasara tare, amman fiye da komai ina taya al'ummar kasashenmu na Habasha da Iritiriya murna."

Akwai kasashen duniya da suka marawa shugaban baya na ganin ya cimma wannan buri wanda a daililin hakan ne a wannan Litinin, sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yake ziyara don ganawa da Abiy Ahmed a birnin Addis Ababa.