1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Amfani da yunwa a matsayin makami a rikicin Tigray

Usman Shehu Usman
June 25, 2021

A sharhunan jaridun Jamus kan nahiyar Afirka a wannan makon jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba rikicin kasar Habasha a sharhinta mai taken amfani da 'yunwa a matsayin makami.

https://p.dw.com/p/3vZjE
Symbolbild Pressespiegel
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

A cewar Firimiyan kasar ta Habasha Abiy Ahmed, babu wata yunwa da ke a yankin Tigray. Firimiyan tamkar dai yana karyata ikitrarin Majalisar Dinkin Duniya wace ta fidda rahoton cewa akwai babbar barazana ta yuwa dake iya hallaka dubban jama'a idann har ba a kai musu dauki ba. A bisa rahoton kwarru na Majalisar Dinkin Duniya kimanin mutane 350 000 na fama da bala'in tamowa. Wasu mutanen kimanin miliyan biyu kuma na dab da fadawa cikin irin wannan matsalar.

Amma ga Abiy Ahmed, yana mai cewa duk wata matsala da ke faruwa a Tigray muna iya magance ta ba tare da sa hannun wani ba. Babu dai wanda ya san hanyar da Abiy zai iya magance lamarin, kuma ba batun bude kofar da masu bukatar taimako za su bi su fice daga yankin don samu tallafi sai dai kawai gwamnati na ci gaba da kai farmakin jiragen sama. Kuma duk wani dan farar hula aka dauke shi a amastayin dan ta'adda.

Äthiopien Tigray-Krise
Hoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

A sharhinta jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba rikicin ta'addanci dake faruwa a yankin Sahel. Ta ce duk da yawan dakarun kasashen Turai da aka jibge a kasashen Nijar da Chadi da Mali da Burkina faso, amma hakan bai hana 'yan ta'adda ci gaba da kai hare-hare ba. Kungiyoyin mayakan har yanzu suna iya kai farmaki kusan duk inda suka tsara kaiwa, kamar yadda ake gani a kasashen Nijar da Burkina Faso da Mali.  

Jaridar Berliner Zeitung

Botsuana | Drittgrößter Diamant der Welt
Hoto: Debswana Diamond Company/REUTERS

Kasar Afirka mafi giman samar da arzikin karkashin kasa na Lu-lu wato Botswana, ta kasance a kanun labarai na kafafen duniya a 'yan kwanakinnan. Hakan ya faru ne yayinda wani dan kasar ya yi arzikin rana guda. bayan yana cikin tunon ma'adinai, kwazam ya samu wata katuwar Lu-Lu'u wace aka ce ita ce ta uku mafi girma a matsayin donkulalliyar Lu'u-lu'u a fadin duniya. Dutsen ma'adinin dai an yi kiyasin ya kai senti meter 7.3 tsawonsa, haka kuma fadinsa ya kai senti meter 5,2. Dama dai mahukuntan kasar Botswana suna cikin kasar Afirka da suka fi samun kudin shiga daga arzikin lu'u-lu'u

BG Wasserverbrauch Anbauprodukte Afrika | Hirse in Simbabwe
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Sai kuma batun da ya shafi noma, wanda shi ma ya dauki hankalin jaridun na Jamus. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ruwaito cewa Afirka ta fara aikin tsare-tsaren noman zamani. Wata sabuwar dabarar noma da aka kirkiro ta fara taimaka wa kananan manoma.

Yawan kayan noma da ake bukata Afirka na matukar karuwa kuma haka ya bada dama ga manoma da ke iya noman zamani cikin sauki. Inda jaridar ta tambayi wani masani, shin ta yaya za a iya taimakawa kananan manoma kimanin miliyan 41 a Afirka yadda za su iya habaka noman da suke yi?

Jaridar na mai cewa domin a cimma wannan burin bawai a iya ciyar da al'ummar Afirka kawai ba, amma a iya kawo ci gaban tattalin arziki, a inganta karkakara su samu tituna, wutar lantarki da sauransu. Bankin duniya dai ya yi kiyasin nan da shekaru tara 9, harkar noma za ta bunkasa da kimanin Dalar Amirka biliyan daya.