1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres ya yi gargadi kan nukiliya

August 8, 2022

Majalisar Dinkin Duniya, ta ja kunnen manyan kasashe a game da kokarin sake komawa ga amfani da makaman nukiliya saboda matukar hadarin da hakan ke da shi ga zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/4FF2p
UN-Generalsekretär Antonio Guterres
Hoto: Pedro Nunes/REUTERS

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce barazana da makaman nukiliya ta sake dawowa bayan samun saukin hakan tsawon shekaru da dama.

Mr. Guterres na fadin haka ne lokacin wani taron manema labaru da ya yi a birnin Tokyo na kasar Japan.

Wannan dai wani martani ne ga hari da aka kai wa tashar makamashin nukiliya mafi girma a nahiyar Turai ta Zaporizhzhya da ke Ukraine.

Jagoran na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce dole ne kasashen duniya su kiyaye amfani da muggan makaman na nukiliya wanda ga dukkan alamu ake kokarin isa gare su saboda hadarin su.

Antonio Guterres dai ya je kasar ta Japan ne domin halartar taro karo na 77 na tunawa da harin da Amirka ta kai da makamin nukiliya a Hiroshima a lokacin yakin duniya na biyu.