1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS ta dakatar da kasar Guinea

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 9, 2021

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO, ta dakatar da Guinea Conakry daga cikinta biyo bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi.

https://p.dw.com/p/40873
Cartoon Guinea Putsch
ECOWAS ko CEDEAO ta dakatar da kasar Guinea saboda juyin mulki

Haka kuma kungiyar ta fitar da wata sanarwa da ke bukatar a gaggauta sako tsohon shugaban kasar Alpha Conde da sojojin suka kame kuma suke tsare da shi, tare da koma wa aiki da kundin tsarin mulkin kasar. Bayan wata ganawa da shugabannin kasashen ECOWAS ko CEDEAO din suka yi, kungiyar ta bayyana cewa za ta tura tawagarta zuwa kasar ta Guinea. A hannun guda kuma Majalisar Dinkin Duniya da Amirka da kungiyar Tarayyar Afirka da ta Tarayyar Turai, sun yi tir da juyin mulkin sojojin a Guinea.