1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu mutane sun rasa ransu sakamakon gobara

Zulaiha Abubakar
June 28, 2018

Mutane uku sun rasa ransu yayin da rukunin wasu gidaje ya kama da wuta sakamkom fashewar wani abu a birnin Bremen na nan kasar Jamus kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta sanar a yau Alhamis.

https://p.dw.com/p/30Tw1
Explosion in Bremer Wohnhaus
Hoto: picture-alliance/dpa/TNN

Wata uwa mai shekaru 41 tare da 'danta mai shekaru bakwai na daga cikin wadanda aka tono gawarwakin su daga cikin 'baraguzan ginin daya rufta sakamkon fashewar abin daya haddasa gobarar,Kakakin hukumar kashe gabora Michael Richartz ta kara da cewa ya zuwa yanzu ba a gano musabbabin al'amarin ba kodayake dai suna zargin iskar Gas.