1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka ta sami karin wa'adi na watanni hudu

Pinado Abdu WabaFebruary 24, 2015

Wakilan kasashen Turan da ke amfani da takardar kudin euro ne suka tabbatar da hakan bayan da suka gana ranar talata da rana

https://p.dw.com/p/1EgdR
Treffen der Eurogruppen Finanzminister Yanis Varoufakis Pressekonferenz
Ministan kudin Girka Yanis VaroufakisHoto: Getty Images/AFP/E.Dunand

Wadanda ke baiwa Girka bashi a kungiyar kasashe masu amfani da takardar kudin bai daya na euro, da ta kunshi kasashe 19 za sun amince da wasikar da ke kunshe da sauye-sauyen da Girka ta ce za ta gudanar domin a kara mata wa'adin samun kudaden ceton da watanni hudu, kuma ana sa ran zai taimaka wajen daidaita kasar da ma hana ta fita daga rukunin kasashen masu amfani da euro.

Da aka tambayi shugaban rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin Mr Jeroen Dijsselbloem ko yana ganin cewa Girka da gaske take yi ga abin da ya kada baki ya ce:

"A gani na da gaske suke, amma ba zai zo musu da sauki ba, wannan ne matakin farko, wannan wasika da suka aiko mana ba sabuwar yarjejeniya ba ce, abubuwan da suke fatan yi ne, ke nan wadanda suke so su maye wa gurbi da wadanda suke so su sauya. zai kuma dauki lokaci a ce an kulla wata sabuwar yarjejeniya"