G7: Putin zai gibi abin da ya shuka | Labarai | DW | 11.10.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

G7: Putin zai gibi abin da ya shuka

Shugabannin kungiyar G7 sun yi Allah wadai da harin makamai masu linzami da Rasha ta kai kan Ukraine, sun kuma ci alwashin ladabtar da Vladimir Putin.

Shugabannin sun ce za su tabbatar Putin ya girbi abin da ya shuka suna masu gargadin cewa zai dandana kudarsa idan yace zai yi amfani da makamai masu guba.

A cikin wata sanarwa kungiyar ta G7 ta ce da kakkausar lafazi tana Allah wadai da harin kan mai uwa da wabi da Rasha ta yi a kan fararen hula wanda ta baiya a matsayin laifukan yaki.

Shugabannin kungiyar sun kuma gargadi Belarus bayan da shugaban kasar Alexander Lukashenko ya sanar da shirin tura sojoji don hadin gwiwa da Rasha.

Kungiyar ta kasashe masu cigaban masana'antu ta duniya G7 ta jaddada goyon bayanta ga yancin Ukraine na kwato dukkan yankunanta da Rasha ta karbe, ta kuma yi alkawarin bata karin tallafi ciki har da karin makamai.