1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Finland ta zama memba a NATO

April 4, 2023

Bayan zaman jira na sama da shekaru 30 kasar Finland ta zama memba na 31 a cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO daga yau Talata.

https://p.dw.com/p/4PfWN
Vor dem Nato-Außenministertreffen
Hoto: Juha Roininen/Lehtikuva/dpa/picture alliance

Shigar Finland cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO na zama wani sabon babi tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar Ukraine.

Za a gudanar da biki na musanman a yau Talata hudu ga watan Aprilu da ke zama ranar zagowar cika shekaru 74 da yankewa kasar ta Finland da ke Arewancin Turai cibiya wacce kuma ke raba iyaka ta sama da kilomita 1.300 da kasar Rasha.

Sakatare Janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya bayyana cewa shigar Finlande cikin kungiyar kawancen tsaron zai kara wa NATO karfi ta ko wacce fuska. Sannan a daya gefe kuma Stoltenberg ya ce yana da yekinin cewa nan zuwa gaba kasar Ukraine ma za ta cika burinta na zama memba a kungiyar amma yanzu ba maganar wannan ne a gaba ba, suna son su ga Ukraine din ta sake dinkewa ta zama kasa daya mai cin gishin kanta.