1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniGabas ta Tsakiya

FIFA ta ce Iran za ta je gasar cin kofin duniya ta Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2026

Sai dai shugaba Donald Trump na Amurka ya yi gargadi da cewa rayuwar 'yan wasan Iran ka iya shiga hadari a kasar.

https://p.dw.com/p/5CGD5
Tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar Iran
Tawagar 'yan wasan kwallon kafar kasar IranHoto: Noushad Thekkayil/NurPhoto/picture alliance

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da cewa Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya ta bana, da za a gudanar a kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico, duk kuwa da dambarwar yakin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban hukumar Gianni Infantino ne da kansa ya ba da wannan tabbaci, yayin taron nazartar harkokin tattalin arziki da kafar yada labarai ta CNBC Amurka ta shirya, yana mai fatan komai zai warware gabanin fara gasar.

Karin bayani:Macron da Starmer za su jagoranci taro kan Mashigin Hormuz

Mr Infantino ya ce wajibi ne Iran ta halarci gasar domin wakiltar al'ummarta, bayan samun nasarar wasannin share fage da suka ba ta wannan dama, la'akari da yadda su ma 'yan wasan ke son bugawa.

Karin bayani:Yakin Gabas ta Tsakiya ya shafi harkokin wasanni

Ko a cikin watan Maris 2026 an jiya Infantino na jaddada irin wannan batu, lokacin da ya halarci wasan sada zumunci da Iran ta buga da Costa Rica a kasar Turkiyya, duk kuwa da ikirarin da shugaban Donald Trump ya yi, na cewa rayuwar 'yan wasan Iran ka iya shiga hadari idan suka je Amurka.

Karin bayani:Jaridun Jamus: Gasar AFCON ta dauki hankali

Wasanni uku na rukuni Iran za ta fafata a biranen Los Angeles da kuma Seattle, yayin da sansaninta zai kasance a garin Tucson na jihar Arizona.