Fashewar wani abu a kamfanin BASF da ke Jamus ya hallaka mutum daya | Labarai | DW | 17.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fashewar wani abu a kamfanin BASF da ke Jamus ya hallaka mutum daya

Akalla mutum daya ya rasu da dama sun jikata sakamakon fashewar wani abu a harabar kamfanin BASF a Jamus.

Fashewar wani abu mai karfi a harabar kamfanin BASF mai harhada magunguna da wasu sinadaran kimiyya da ke a garin Ludwigshafen na nan Jamus, ta yi sanadin mutuwar akalla mutum guda sannan ta jikata mutane da yawan gaske yayin da wasu suka bata. Kamar yadda kamfanin ya fada a cikin wata sanarwa, yanzu haka ma'aikatan ceto daga yankin gaba daya suna aiki tukuru don shawo kan lamarin. Hatsarin ya auku ne a cikin wani bututun tura magunguna da sauran sinadarai daga jiragen ruwa zuwa ainihin wuraren da ake sarrafa su. Saboda dalilai na tsaron lafiya, kamfanin ya kashe sauran injunansa da ke a wannan haraba.