Zirin Gaza: Fargabar kisan kiyashi
October 15, 2023Kungiyar Kasashen Larabawan da takwararta ta Tarayyar Afirka AU sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da al'ummomin kasa da kasa da su yi duk mai yiwuwa wajen dakatar da rikicin kafin lokaci ya kure. Kiran nasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU 27 suka kara jaddada 'yancin Isra'ila na kare kanta karkashin dokokin kasa da kasa da kuma na jin-kai, biyo bayan harin ba-zatan da Hamas ta kai mata da suka yi kakkausar suka a kansa. A hannun guda kuma Isra'ilan ta dawo da ruwan sha a yankin kudancin Zirin na Gaza da ta katse a baya, yankin da ta bukaci miliyoyin Falasdinawa mazauna Gazan su koma. Ministan makamashi na Isra'ilan Israel Katz ya bayyana cewa, matakin dawo da ruwan zai tilasta Falasdinawan yankin Zirin Gazan komawa kudancin da suka bukace su tun da farko.