Farautar maharan Paris a Beljiyam | Labarai | DW | 23.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farautar maharan Paris a Beljiyam

'Yan sandan kasar Beljiyam na ci gaba da samame a birnin Brussels, a kokarin da suke na kamo wadanda ake zargi da hannu a kitsa harin ta'addancin da aka kai birnin Paris na Faransa.

Farautar maharan Paris a birnin Brussels na kasar Beljiyam

Farautar maharan Paris a birnin Brussels na kasar Beljiyam

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan sandan sun sake cafke wasu mutane biyar yayin da suka tsare da wasu 16, inda kuma birnin ke ci gaba da zama cikin dokar ba shiga ba fita, a kokarin da suke na farautar wadanda ake zargi da harin na Paris ciki kuwa har da na kan gaba a zargin wato Salah Abdeslam. A hannu guda kuma Firaministan Birtaniya David Cameron ya shaidawa shugaban kasar Faransa Francois Holland cewa zai nemi amincewar majalisar dokokin Birtaniyan domin shiga a dama da kasarsa a hare-haren taron dangi da jiragen yaki ke kai wa a kan 'yan ta'addan IS a Siriya. Harin na birnin Paris dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 130, yayin da wasu da dama suka jikkata.