Faransa za ta taimakawa yaki da Boko Haram | Labarai | DW | 11.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta taimakawa yaki da Boko Haram

Ministan tsaro Jean-Yves Le Drian ya ce Faransa zata kara yawan sojojinta a yankin Yammacin Afrika domin tallafawa sojojin da ke yakar Boko Haram.

Ya ce karin sojojin nasu wani mataki ne na taimakawa shawo kan tashe- tashen hankula da ya mamaye kewayen Tabkin Chadi, daura da haka bai yi wani karin bayani ba.

Tun a farkon wannan shekarar ce dai sojojin Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Benin, suka fara taimakawa takwarorinsu na Najeriya a kokarinsu na kawo karshen mayakan tada kayar baya na Boko Haram, bayan da kungiyar ta karbe madafan ikon wasu yankunan kasar d, tare da fara kaddamar da hare hare akan garuruwan dake kan iyakokin kasashe makwabta.

A yanzu haka dai Faransa na da adadin sojojinta 3,000 a yankin, banda wasu dakaru na musamman, wadanda ke jibge a Mauritaniya daga yammaci zuwa kudancin Libiya, wadanda aka dorawa alhakin farautar mayakan kungiyar Alqaeda.