Faransa za ta fadada kasuwancinta da Najeriya | Siyasa | DW | 15.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Faransa za ta fadada kasuwancinta da Najeriya

'Yan kasuwar Faransa sun jaddada kudurinsu na fadada harkokin kasuwanci da Najeriya daidai lokacin da shugaban Najeriya ke ziyara a Paris.

A karon farko a nahiyar Afirka kungiyar MEDEF da ke wakiltar 'yan kasuwar kasar Faransa a matakin kasa da kasa wacce kuma ke da kamfanoni dubu 800 a karkashinta a kasashen duniya ta bayyana aniyarta ta shiga Najeriya don tallafawa tattalin arziki. Wannan kungiyar dai ta bayyana hakan ne a rana ta biyu ta ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari ke yi a birnin Paris na Faransa.

Paris Medef Zentrale Buhari Gattaz

'Yan kasuwar Faransa na son zuba jari a fannin wutar lantarki don bunkasar kasuwanci a kasar

'Yan kasuwar dai sun yi wa Najeriya wannan albishir din ne daidai lokacin da tawagar shugaba Muhammadu Buhari da ke ziyara a kasar ta gana da su inda suka ce suna da niyar zuba jari a Najeriyar kamar yadda Malam Garba Shehu mai bada shawara kan lamuran yada labarai ga shugaba Buhari ya bayyana, har ma ya ke cewar ''za su fadada harkokinsu na zuba jari da ma zuba sabbin hannayen jari a fannoni daban-daban na tattalin arzikin Najeriya"

Fannin matsalar wutar lantarki na cikin matsalar da ke damun Najeriyar musamman ga masana'antu wadda a cewar Malam Garba Shehu shi ma fannin ne da zai samu zuba jari karkashin kamfanin Lafarge wanda sannanen kamfani da ke samar da Siminti amma a wannan karon zai mai da hankali ne kan lantarki da ake samu daga hasken rana kuma tawagar 'yan kasuwar Faransa za su ziyarci Najeriya cikin watan Oktoba don cigaba da zantawa kan wadannan batutuwa.

Nigeria Boko Haram Terrorist

Faransa na son bada tallafinta wajen ganin an kawar da kungiyar Boko Haram.

Baya ga batun kasuwanci, Shugaba Francois Hollande a jiya Litinin (14.09.2015) ya yi alkawarin cigaba da dafawa Najeriya a yunkurinta na kawar da 'yan ta'adda musamman ma 'yan kungiyar nan ta Boko Haram a wata zantawa da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari. Masu sharhi kan harkokin da suka danganci Afirka dai sun fara tofa albarkacin bakinsu kan ziyarar ta Buhari a Faransa har mutane irin su Sadiq Abba dan jarida mazaunin birnin Paris ya ke ganin tallafawa Najeriya daidai ya ke da tabbatar da cigaban Afirka duba da matsayin Najeriya a nahiyar.

Sauti da bidiyo akan labarin