1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa ya ce duniya ta shiga yaki

Suleiman Babayo ZMA
February 26, 2022

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya nemi duniya ta shirya ganin yaki na tsohon lokaci sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine lamarin da ya janyo mutuwar mutane kusan 200.

https://p.dw.com/p/47eGI
Kombobild Russland Frankreich Putin und Macron
Hoto: AFP

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya ce duniya ta shirya ganin yaki na tsohon lokaci sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar a kan Ukraine. Sannan shugaban ya bukaci a shirya bisa wannan yanayin da duniya ta samu kanta a ciki.

Macron ya fadi haka a wajen bikin baje kolin kayan amfanin gona na kasar mai tasiri, amma ya katse ziyarar sakamakon abin da yake faruwa na kutsen na Rasha a Ukraine, inda ya ce Turai tana tare da mutanen Ukraine.

Faransa ta nuna tsoron 'yan aware a kasashen tsohuwar Tarayyar Soviet da ke dasawa da mahukuntan Rasha, za su tayar da kayar baya domin neman Rasha ta kawo musu dauki, lamarin da zai zurfafa zaman tankiya da ake ciki.