SiyasaTurai
Faransa da Canada za su bude ofisoshin jakadanci a Greenland
February 6, 2026
Talla
Kasashen Faransa da Canada da ke tsantsar adawa da matakin shugaban Amurka Donald Trump na karbe iko da Greenland za su bude kananan ofisoshin jakadanci a Juma'ar nan a Nuuk babban birnin yankin, a wani mataki na karfafa gwiwa ga Denmark da tsibirin ke karkashinta.
Wannan mataki na kasashen biyu alama ce ta nuna wa Trump 'yar yatsa kan cewa kasashen Turai da aminansu na tare da Denmark kuma ba za su lumunci shirinsa na kwace yankin Greenland ba.
Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da Trump da sakataren kungiyar tsaro ta NATO da kuma mahukuntan Denmark ke tattaunawa kan wani shiri da ya jibanci makomar Greenland duk da cewa fadar mulki ta Copenhague ta hau dokin naki kan matakin Washington na karbe iko da yankin mai kwarya-kwaryar 'yanci.