Fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta | Labarai | DW | 06.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Rasha da Turkiyya ta soma aiki a yankin Idlib, biyo bayan ganawar da shugabannin kasashen biyu suka yi a birnin Moscow.

Rahotanni daga yankin Idlib na kasar Siriya sun tabbatar da cewa yarjejeniyar da Turkiyya da Rasha suka cimma ta tsagaita buda wuta ta soma aiki a yau Jauma'a 06.03.2020 a wani yunkuri na dakatar da gumurzu takanin dakarun Siriya masu goyoyn bayan Rasha da na Turkiyya.

Kungiyar kare hakin bil'Adama mai sa ido kan harkoki a kasar ta Siriya ta tabbatar da soma aiki da kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar bangarorin suka cimma a yankin Idlib.

A yammacin jiya Alhamis ne dai shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan suka gana tare da bayyana matakin yin aiki tare don kaucewa fito na fito a Siriya inda daga bisani suka sanar da cimma yarjejeniyar a lardin na Idlib da ke arewa maso yammacin Siriya.