Fafutukar kwato ‘yan mata da aka sace | BATUTUWA | DW | 13.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Fafutukar kwato ‘yan mata da aka sace

Kungiyar Bring Back Our Girls da ke fafutukar kwato ‘yan matan da ‘yan Boko Haram suka sace sun bai wa gwamnati wa’adin kwanaki bakwai ta kwato ‘yan matan Daptchi 110 ko kuma su kai gwamnatin kara kotu.

Sun dai ba da jerin tambayoyi har guda 14 da suke son gwamnatin ta ba da amsa da suka hada da batun zargin sakaci da nuna hali na ko in kula bisa yadda al’amarin ya faru da ko da harsashi guda ba a harba ba balle a yi batun farmaki na bin sawu. Mrs Obi Ezekwesili ita ce shugabar wannan kungiyar, ta bayyana matakin da za su dauka bayan cikar wa’adin na kwanaki bakawai na shigar da kara saboda sakaci.


Tuni dai kungiyar ta dauki kwararren lauya Femi Falana da zai jagorance su zuwa kotu domin kalubalantar gwamnati bisa zargi na sakaci a kan sace ‘yan matan na Dapchi. Wannan ne dai karon farko da kungiyar ta bayyana shirin matakin shari’a kan batun na ‘yan matan Chibok da na Dapchi. Za a saka ido a ga tasirin da wannan zai yi wajen sako 'yan mata da gwamnati ta ce ta na tattaunawa da ma samar da tsaro ga sauran da suke makarantu a kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin