Eu zata tallafawa wasu kasashe 10 na Afrika | Labarai | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Eu zata tallafawa wasu kasashe 10 na Afrika

Kwamishinan bada tallafin raya kasa na kungiyyar gamayyar turai, wato Louis Macheal, yace hukumar zartarwar kungiyyar ta amince da kudurin bawa wasu kasashe na Afrika 10, tallafin yuro miliyan 165 da digo 7.

Wadannan kudade a cewar hukumar zartarwar ta Eu, za ayi amfani dasu ne a matsayin tallafi, ga miliyoyin mutanen da bala´oi iri iri suka afkawa sakamakon igiyar ruwan ta tsunami da kuma dangogin ta.

Kasashen da zasu amfana da wannan tallafi a cewar , kwamishinan bada tallafin raya kasa na kungiyyar ta Eu,sun hadar da Burundi da chad da Comoros da Congo da kuma Ivory Coast.

Ragowar sun hadar da Liberia da Madagascar da Sudan da Tanzania da kuma Uganda.