EU zata fadada ayyukan tsaro a yankin Rafah | Labarai | DW | 13.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU zata fadada ayyukan tsaro a yankin Rafah

Kungiyar tarayyar ta zartar da cigaba da aikin tsaronta a kann iyakokin zirin Gaza da Masar,wadda ke zama hanya daya da palasdinawa keda sukunin hulda da kasashen waje ba tare dabin ta cikin Izraela ba.A taron da suka gudanar yau a birnin Brussels din kasar Belgium,Ministocin harkokin waje na turan sun fadada ayyukan tsaro dake gudana garin Rafah,na tsawon watanni shida ,tare da kira ga izraela data tabbatar da barin hanyar a bude.A karshen wannan watan nedai aikin tsaron dakarun EU din ke karewa,kuma izraela ta nemi sake tattauna batun waadin,domin zargin palasdinawa da yin smuggan makamai ta wannan hanya.Tun bayan da sojojin sakai na yankin Palasdinawa suka sace jamiin sojin Izraela a kwatan yuni nedai,ta matsa kaimi wajen rufe wannan kann iyaka,wanda ke dada jefa alummomin palasdinun cikin halin kakanikayi na rayuwa.