EU za ta samar da likitoci 5,000 don yaki da Ebola | Labarai | DW | 26.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU za ta samar da likitoci 5,000 don yaki da Ebola

Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ta bukaci da a samar da likitoci don yaki da wannan annoba ta Ebola mai saurin kisa da ta addabi kasashen yammacin Afirka.

G20 Australien Jean-Claude Juncker 15.11.2014

Jean-Claude Juncker Shugaban hukumar EU

A cewar majiyar da ta yi magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ta kara da cewa manyan jami'an hukumar ta EU na tuntubar kasashen da ke karkashin kungiyar ta yadda za su shiga aikin bada wadannan jami'ai. Majiyar ta ce akwai ma bukatar dubban ma'aikatan kula da lafiya da ake sa ran za su shiga wannan tafiya. Shi ma da yake jawabi a shafinsa na Twitter Vytenis Andriukaitis kwamishina na harkokin kiwon lafiya a kungiyar ta EU ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ya sami damar tuntubar ministocin kiwon lafiya na kasashe 14 na kungiyar, inda ya bukaci da su tura jami'an lafiya zuwa kasashen da suke fama da wannan annoba ta Ebola. Ya ce akwai nasara kan irin amsoshin da ya ke samu, sai dai bai bada cikakken bayaniba.