EU ta yi watsi da sakamakon zaben Venezuela
August 1, 2024Talla
Babban jami'in diflomasiya na kungiyar Tarayyar Turai EU, Josep Borrell ya ce hukumar zaben Venezuela ta bayyana sakamakon ne bayan kirga kashi 80 cikin 100 na kuru'u.
Karin bayani: Venezuela: Shugaba Maduro ya lashe zabe karo uku
Ya kara da cewa, sakamakon zaben da bangaren adawa suka gabatar ya sha bambam da na hukumar. A ranar Larabar ne, shugaba Maduro ya sha alwashin cewa, bangaren adawa ba zai taba mulkar kasar ba. Batun da ke ci gaba da jawo suka kan sahihancin zaben da haifar da zanga-zanga da ta bar baya da kura.
A kalla mutane 11 ne aka tabbatar da mutuwarsa sakamakon zanga-zangar kan zaben da ake zargin an tafka magudi.