EU za ta dauki mataki kan shugaban Venezuela
August 2, 2017Yunkurin daukar matakin a kan Nicolas Maduro da kungiyar Tarayyar Turai ta yi, ya biyo bayan zargin cewa gwamnatinsa ce ta bayar da umarnin tsare wasu 'yan adawa biyu da suka furta kalaman da ba su yi wa shugaban dadi ba, mai magana da yawun kungiyar ta EU ta ce ana can ana ganawa da wakilan mambobin kasashen kungiyar don duba matakan da ya dace a dauka kan ladabtar da masu hannu a gallazawa al'umma a yayin rikicin zaben kasar, a ranar Litinin da ta gabata Amurka ta sanar da sanyawa shugaba Maduro takunkumi inda ta kwace kaddarorinsa tare da hana Amurkawa yin mu'ammala ta cinnakaya da kasar
Zaben majalisar kula da tsarin mulki da aka gudanar a kasar ta Venezuela ya bar baya da kura, ana zargin an tafka magudi inda hukumar zaben kasar ta fidda sanarwa da ke nuni da cewa akwai kuri'u kimanin miliyan guda da aka yi aringizonsu, akwai kuma batun tauye hakkin fadin albarkacin baki inda aka yi ta kama masu adawa da gwamnati mai ci, yanzu haka ma 'yan adawa a kasar sun sanar da dage zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a wannan Laraba a Caracas babban birnin kasar zuwa gobe Alhamis, domin ta zo daidai da ranar da za a kaddamar da abin da suka kira sabuwar haramtacciyar majalisar dokoki wacce za ta bai wa Shugaba Nicolas Maduro karin karfin iko.