1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta ce ana bukatar gyara a tsarin zaben Najeriya

June 15, 2019

A wani abin da ke zama koma baya ga fatan Najeriya na samar da ingantaccen zabe, masu sa ido na Kungiyar Tarayyar Turai suka ce ana bukatar gyara sosai a kan hanyar kaiwa ga biyan bukatar 'yan kasar cikin harkokin zabe.

https://p.dw.com/p/3KWKi
Nigeria Präsidentschaftswahlen Schlange vor Wahllokal
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

 

Sun share tsawon watanni uku suna kallon shirin aiwatar da zabukan tarrayar Najeriyar da aka kammala cikin watan Afirilu, kuma 'yan kallon na EU kusan 91 sun ziyarci sako da lunguna na tarrayar Najeriyar da nufin kallon tsarin. Sai dai sun ce ana bukatar jan aiki a bisa hanyar tabbatar da ingantaccen tsarin zaben da a cewarsu ke da babbar matsala.

Cikin wani jawabin karshe na sakamakon kallon zaben, shugabar tawagar 'yan kallon Turai Maria Arena ta ce sun bada shawarwari har guda 30 da suka shafi tsarin zaben, da tsaronsa da kuma rawar kafafen labarai. Akwai  kura-kurai da daman gaske, sannan kuma an gaza aiwatar da sauye-sauyen da aka alkawarta a lokacin zaben 2015 yayin zaben na 2019 abin da ya haifar da matsaloli. A tunanin Arena ana bukatar kwaskwarimar da za ta samu jagorancin shugabanci na siyasa da kuma tattaunawar da za ta kunshi masu ruwa da tsaki a cikin harkokin zaben.

Karikatur: Nigeria Wahl Hooligans
'yan daba sun haifar da tseko a zaben 2019 a NajeriyaHoto: DW

  Ta ce "Hukumar INEC ba ta buga daukacin sakamakon zabe na unguwanni bayan kammala zabe ba, saboda haka da kamar wuya ga jam’iyyu da 'yan takara da ma 'yan zaben su iya tabbatar da sakamakon zaben a kashin kansu ba. A saboda haka 'yan kallon Turai na bada shawarar kara karfin hanyoyin tara sakamakon zaben na hukumar domin kara musu karfi.”

Rawar jami’an tsaron ta bata ran 'yan kallon EU da suka ce hakan har ya kai ga shafar martabar tsarin zaben Najeriya. INEC ta bada rahoton kai hari kan jami’anta da ragowar turawan zabe. Ta ce sojoji da 'yan daba sun kai hari kan cibiyar tara sakamakon zaben a jihar Rivers a lokacin zabe na gwamnan jihar.

Duk da cewar 'yan kallon sun ce ba su da hurumin yanke hukunci a kan sahihancin sakamako dama kyawun zaben a bisa wadanda suka gabaceshi, amma su tabbatar da sauyin da ake bukata a gani a kasar ya kai har ga kafafen yada labaran da a cewarsu ba su da damar daidaito da tabbatar da adalci a tsakanin daukacin masu takarar. Tsadar kafafen labaran game da tsadar izini na kafasu, ya sa banda shugaban kasa sai gwamnonin da suke kai ne kadai suke da damar da ajisu a yayin yakin neman zabe a cewar Maria Arena.