EU :Nan gaba kadan ne za a janye wa Iran takunkumi | Labarai | DW | 11.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU :Nan gaba kadan ne za a janye wa Iran takunkumi

Kantomar manufofin Kungiyar Tarayyar Turai Federica Mogherini ta bayyana cewar kungiyar bata da wani tartibin lokaci da aka ajiye don janyewa Iran takunkumi.

Federica Mogherini ta yi nuni da cewar aiwatar da yarjejeniyar na tafiya kamar yadda aka tsara,kana abin karfafa gwiwa ne,na yi magana ta wayar tarho a kan batun da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif kwanaki kalilan da suka wuce da kuma John Kerry jiya abubuwa na tafiya dai-dai don haka muna ganin nan gaba kadan za a fara aiwatar da shirin janye kakunkumin.

Iran ta tsimma yarjejeniya ce kan makaman nulikiyar ta ne da kasashe biyar na yammacin duniya a shekarar da ta gabata a bisa sharadin musayar janye mata takunkumin da aka sanya mata wanda ya da kushe tattalin arzikinta.