Eu na kokarin dakile kwararowar bakin haure | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Eu na kokarin dakile kwararowar bakin haure

Wasu Jami`an kungiyyar hadin kann turai sun shirya gabatar da wani kuduri na duba yiwuwar samar da jiragen ruwa dana sama don amfani dasu, wajen sintirin hana bakin haure shigowa izuwa nahiyar turai.

A cewar kwamishinan kungiyyar ta Eu mai kula da harkokin cikin gida wato Franco Fratini,gabatar da wannan bukata ya zama dole don ganin an hana bakin haure daga nahiyar Africa shigowa izuwa nahiyar turai.

Rahotanni dai sun rawaito Mr Franco Fratini na cewa zai gabatar da wannan shawarar ne, a yayin wani taro da kungiyyar zata gudanar na kwanaki biyu a birnin Dresden na kasar Jamus.

Ya zuwa yanzu dai tuni mai masaukin baki, waato ministan cikin gida na Jamus, Wolfang Schäuble,ya nuna muhimmancin amincewar da wannan shawara daga bangaren yayan kungiyyar ta Eu.