1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU amince da sabuwar dokar mallakar fasaha

Abdullahi Tanko Bala
March 26, 2019

'Yan majalisar dokokin Turai sun amince da dokar mallakar fasaha da za ta tilastawa kamfanoni kamar Google da Youtube biyan mawallafa idan sun yi amfani da abin da suka wallafa.

https://p.dw.com/p/3FgVd
Berlin Proteste gegen EU-Urheberrechtsreform
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Majalisar dokokin Turai a wannan talata ta amince da kudirin doka mai sarkakakiya da aka yiwa kwaskwarima ta mallakar fasaha wadda mawallfa da masu kasuwancin wakoki suka bukata wadda kuma ta sha suka daga kamfanonin fasaha da na internet.

Sabuwar dokar za ta maye gurbin wadda ake amfani da ita tun shekarar 2001.

Gyaran da aka yiwa kundin dokar dai na nufin cewa daga yanzu wajibi ne shafukan Internet kamar Google da Youtube da Facebook su biya mawallafa idan wani ya yi amfani da labaran da aka wallafa a shafukansu.

Masu sukar lamirin dokar na cewa hakan zai tauye 'yancin amfani da kafar Internet sannan kamfanonin za su dauki matakin tace dukkan wani abu da za a iya daukowa daga shafukan nasu.