Google kamfani ne da jama'a ke amfani da shi wajen neman bayanai a shafukan intanet. Wannan ne ya sanya ake masa lakabi da ''shafin matambayi ba ya bata''.
Larry Page da Sergey Brin ne suka kirkiri shafin Google lokacin da suke karatunsu na digiri na uku a jami'ar Stanford da ke Amirka. Shafin Youtube na kallo da musayar bidiyo da kuma manhajar wayar komai da ruwanka ta Android na daga cikin irin abubuwan da ke karkashin kamfanin Google. Dubban miliyoyin mutane ne a duniya ke amfani da Google.