Google da Facebook sun tilasta rigakafin corona | Labarai | DW | 29.07.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Google da Facebook sun tilasta rigakafin corona

Kamfanonin internet na Google da Facebok sun umurci ma'aikatansu a Amirka da yin allurar rigakafin COVID kafin su koma aiki a cikin ofis, domin kare sabon nau'in corona na Delta.

Kamfanonin guda biyu sun dauki wannan mataki ne ba tare da shawarartar juna ba, sai dai Google ya ce dokar za ta shafi ma'aikatantan  da ke Amirka ne kadai a yanzu kamin daga baya a fadada dokar zuwa sauran yankuna a watanni masu zuwa.

Matakin tilasta ma'aikata allurar na zuwa ne sakamakon yaduwar sabon nau'in annobar corona mai suna Delta, sai dai Google na jan kafaka na dawo da ma'aikata aiki a ofis har zuwa tsakiyar watan Oktoba.

Amma kamfanin Apple na kan bakansa na barin ma'aikatansa ci-gaba da aiki daga gida, kuma babu niyyar tilasta su yin allurar rigakafin corona.