Apple kamfani ne da ke kera wayoyin hannu da na'urar kwamfiyuta da sauran abubuwa da suka dangaci nau'in sadarwa irin na zamani.
Kamfanin Apple wanda ke da cibiyarsa a Amirka na daga cikin kamfanonin da suka yi fice a duniya sai dai ya na shan suka sosai daga masu amfani da kayansa da kuma masu kare hakkin sayen kayayyaki. Har wa yau ana sukar kamfanin kan irin rawar da ya ke takawa wajen gurbata muhalli.