Dambarwar haraji tsakanin Apple da EU | Labarai | DW | 30.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dambarwar haraji tsakanin Apple da EU

Kungiyar tarayyar Turai ta umarci kamfanin kera na'urar sadarwa na Apple ya biya tsabar kudi euro biliyan goma sha uku na harajin ga Ireland.

A jerin hukunce hukunce na baya bayan nan da suka harzuka Washington, hedikwatar tarayyar Turan a Brussels ta ce kamfanin na Apple ya kaucewa biyan haraji a kusan dukkanin ribar da ya samu a karkashin yarjejeniyar ta Dublin. Kwamishiniyar kungiyar tarayyar Turai mai kula da kula da gogayyar cinikayya Margrethe Vestger ta yi bayani da cewa O-Ton.....

" Tace domin maido da adalci a gogayyar cinikayya wajibi ne Apple ya biya kudi kimanin euro biliyan goma sha uku har da kudin ruwa na harajin da bai biya ba ga kasar Ireland."

Apple din da gwamnatin Ireland sun ce sun ce za su daukaka kara a kan hukuncin na hukumar tarayyar Turai. Yayin da ma'aikatar kudi ta Amirka ta ce hakan zai yi nakasa dangantakar tattalin arziki tsakaninta da kungiyar tarayyar Turai.