EU: Takaddama a kan harajin cinikayya | Labarai | DW | 15.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

EU: Takaddama a kan harajin cinikayya

A wannan Larabar ce kotun tarayyar Turai mai daraja ta biyu ta soke hukuncin da ya baiwa kamfanin latironi na Apple umurnin mayarwa kasar Ireland harajin Euro biliyan 13.

Kotun ta bai wa kamfanin Apple da Ireland nasara a karar da suka shigar a shekarar 2016 wanda ta ce ba sai kamfanin mallakin kasar Amurika ya biya wannan kudin ba.

Alkalan kotun a Luxemburg sun ce kotun ta yanke wannan hukuncin ne saboda kungiyar tarayyar Turai ta gaza bayar da gamsassun bayanai na doka da suka nuna samun fifiko a gogayyar cinikayya.

Wannan hukunci dai ka iya kai wa ga mataki na gaba na daukaka kara zuwa kotun koli ta tarayyar Turai.