1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tilasta Google sake sharuda a Faransa

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2022

Kotu ta ci tarar kamfanin Google na Amirka biyan tarar yuro miliyan biyu saboda cin mutuncin harkokin kasuwanci tare da takurawa kanan kamfanoni. An umarci kamfanin ya gyara wasu sharuda bakwai a cikin kwangilolinsa.

https://p.dw.com/p/49CKh
Google, taswira
Hoto: Andre M. Chang/ZUMA Press Wire/dpa/picture alliance

Alkalan wata kotu a binrin Paris sun umarci kamfanin Google ya sake rubuta kwangilolin da yake amfani da su ga masu habaka manhajojin zamani wato "apps developer', bayan da la'akari da cewa kamfanin na kakaba haraji kan kananan kamfanoni.

kamfanin Google ya tilasta wa masu habaka ayyukan fasaha biyan wasu harajin dole har kashi 30 cikin 100 daga kowane tallace-tallace a kan manhajar Play Store.

Alkalan kotun sun baiwa Google watanni uku ya canza sharudan kwangilolin, Google ya ce ya riga ya canza wasu sharuddan kuma tuni ya takaita tasirinsa ga kananan masu fasaha.

Kamfanonin Google Facebook na fuskantar matsin lamba a kasashen duniya musamman Turai saboda zargin cin hanci da rashawa da kuma keta ka'idojin sirrin bayanai.