Erdogan na ziyara a Afirka ta Yamma | Labarai | DW | 29.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erdogan na ziyara a Afirka ta Yamma

An shiga yini na biyu na ci gaban ziyarar da Shugaban Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya soma a wasu kasashen Afirka da suka hada da Cote d'Ivoire Najeriya Ghana da Guinea.

A wannan Litinin ce aka shiga yini na biyu na ci gaban wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya soma a jiya Lahadi a kasar Cote d'Ivoire a matakin farko na wata ziyara da yake shirin kai wa a wasu kasashen Afirka ta yamma da suka hada da Najeriya da Ghana da kuma Guinea.

Fadar shugaban Turkiyyar ta ce makasudin wannan ziyara dai shi ne karfafa huldar diplomasiyya da ta harakokin kasuwanci tsakanin Turkiyyar da kasashen yankin. Shugaban Erdogan na wannan ziyara tasa ce tare da rakiyar tawagar wasu gwamman shugabannin kamfanoni da manyan 'yan kasuwar kasar tasa wadanda za su halarci wani babban taro kan tattalin arziki a birnin Abijan.

Adadin kudaden da Turkiyyar ta zuba jari a kasar ta Cote d'Ivoire ya karu daga miliyan 150 na Dallar Amirka a shekara ta 2008 zuwa miliyan 390 a shekara ta 2015.