Erdogan: Ko dai mu hade da Turai ko a ware | Labarai | DW | 02.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Erdogan: Ko dai mu hade da Turai ko a ware

Wannan kalamai na Shugaba Erdogan dai na zuwa ne bayan da kwamishinan Kungiyar Tarayyar Turai Johannes Hahn ya ce Turkiya ta koma baya a shirin hadewa da Kungiyar EU.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya bayyana a ranar Talatan nan cewa Kungiyar Tarayyar Turai na da zabi guda biyu: ko dai kungiyar ta bude sabon babi na shigar kasar cikin kasashen na Turai  ko kuma mahukuntan na birnin Ankara sun zabi raba gari, kasancewar ba su da wani abu da za su tattauna da kungiyar ta EU.

Wannan kalamai na Shugaba Erdogan na zuwa ne bayan da kwamishina daga Kungiyar Tarayyar Turai Johannes Hahn da ke nazari kan batun bukatar ta Turkiya na shiga Kungiyar EU ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Turkiya karkashin Erdogan ta koma baya a dangane da batun shiga cikin kasashen na EU.

A cewar Erdogan a bikin sake komawarsa jam'iyya mai mulki ta AKP, daga wannan lokaci babu abin da ya yi saura face a bude kofofi da suka rage ko kuma su yi bankwana da juna.