Ebola ta hallaka fiye da mutane 3000. | Labarai | DW | 28.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola ta hallaka fiye da mutane 3000.

Annobar cutar Ebola dake wakana a wasu kasashen yammacin Afirka, ta kashe fiye da mutun 3000 daga cikin 6.500 da suka kamu da wannan cuta.

A sakamakon baya-bayannan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar, adadin wadanda suka rasun ya karu ya zuwa mutun 3.093 a cikin kasashen. A kasar Laberiya inda cutar tafi kamari, ta kama mutane a kalla 3.458, daga cikin su 1.830 suka rasu kawo yanzu, sannan a kasar Saliyo cutar ta Ebola ta kama mutane 2.021 inda daga cikin su mutane 605 suka rasu a cewar hukumar, yayin da a Tarayyar Najeriya mutun takwas ne suka rasu daga cikin 20 da suka kamu da cutar ta Ebola.

Ana kamuwa da wannan cuta ta Ebola ce ta hanyar gama jiki da wanda ke dauke da cutar, ko taba jinin sa, ko wani ruwa da ya fita daga jikin mai cutar ta Ebola, kuma cutar tana iya bayyana a jikin mutun daga kwanaki biyu, zuwa makonni uku, sannan mai Ebola na iya kasancewa babban hadari ga wanda bashi da ita da zaran cutar ta fara bayyana a jikin sa.

Mawallafi:Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu