Ebola: Gini ta rufe iyakarta da Saliyo | Labarai | DW | 30.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola: Gini ta rufe iyakarta da Saliyo

Gini ta sanar da rufe iyakokinta da kasar Saliyo na tsawon kwanaki 45 a wani mataki da ta ce ta dauka don dakile shigar cutar Ebola cikin kasar.

To sai dai al'ummar kasar da dama sun koka game da wannan mataki da shugaban kasar Alpha Conde ya dauka a karshen mako don a cewarsu an shammace su kansacewar mutane da yawa sun ketare cikin Saliyo musamman Freetown, wanda rufe iyakokin ba zai bari su koma gida ba.

Wata mata da yaranta biyu da ke kokarin komawa Gini din daga Saliyo ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewa jami'an tsaro sun hana su komawa gida Gini wanda hakan ka iya jefa su cikin matsala.

Dama dai a watannin baya Gini din kamar Saliyo da cutar ta Ebola ta yi wa ta'annaki ta dauki irin wannan matakin don magance yaduwar cutar daga yankunan da ta bulla a kan iyakokin kasashen biyu.