Ebola: Dokar hana fita a Saliyo ta fara aiki | Labarai | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ebola: Dokar hana fita a Saliyo ta fara aiki

A wannan Juma'ar ce dokar hana fita ta kwanaki ukun da gwamatin Saliyo ta sanya da nufin yakar cutar nan ta Ebola za ta fara aiki a dukannin yankunan da ke kasar.

A tsawon wannan kwanakin ministan watsa labaran kasar Alpha Kanu ya ce jami'an kiwon lafiya za su bi gida-gida don fadakar da al'umma kan matakan kare kai daga kamuwa da cutar da ma zakulo wanda cutar ta kama don yi musu magani.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce kimanin ma'aikata 30 talatin ne za su kewaya kasar don gudanar da wannan aiki, inda hukumomi ke cewar in har al'umma suka amsa wannan kira to matakin zai taimaka matuka wajen rage bazuwar cutar wadda ta yi sanadin rasuwar mutane da dama a kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo